• 18 Jun, 2025

Ya Zama Dole Mu Tashi Tsaye Mu Ceto Arewa—Cewar Gwamna Bala Mohammed

Ya Zama Dole Mu Tashi Tsaye Mu Ceto Arewa—Cewar Gwamna Bala Mohammed

1000005241.jpg

Gwamnan jihar Bauchi Bala Mohammed ya ce, kowa yasan arewacin Najeriya da hadin kai duk da cewar yankin na fama da matsalar rashin tsaro.

Bala Mohammed ya ce sakamakon matsalar rashin tsaro, yan arewa ba sa iya ci da kansu, ga kuma matsalar rashin aikin yi tsakanin matasan yankin.

Mohammed ya kalubalanci gwamnonin arewa ta hanyar tambayarsu gudumawar da su ke bada wajen warware matsalolin yankin.

Gwamna Bala Mohammed ya ce matsalolin da arewa ke fuskanta sun wuce tunanin mutum. Matsalolin sun ta'azzara matuka.

Bala Mohammed ya kara da cewa mafi yawancin yankunan arewa sun dogara ne da gwamnatin tarayya wajen samun kudin shiga, duk da mafi yawancin manyan Najeriya yan yankin ne.

Gwamnan Bauchin ya ce arewa ce koma baya a harkar ilimi wanda shi ne kashin bayan tunani mai nagarta.

Gwamnan ya kara da cewa babu jituwa tsakanin manyan arewa da talakawan yanki, bugu da kari, malaman addini sun dasa kiyayya tsakanin shugabanni da talakawan yankin, da ma sauran matsaloli da dama da ke addabar arewa.

Bala Mohammed ya ce, Allah ya wadata arewa da duk albarkatun kasa kama daga zinari, azurfa, danyen mai, iskar gas da kasa mai albarka na noma.

Duk da haka, har yaryanzu arewa na dogara da gwamnatin tarayya maimakon dogaro da kanta.

Bala ya kara da cewa, babu albarkatun kasa da babu a jihar Bauchi da ma sauran jihohin arewacin kasar, amma shugabannin sun gaza gano zaren amfana da wadannan albarkatun domin kawo canji a arewa.

Ahmed Abubakar

How puzzling all these changes are! I'm never sure what I'm going to turn into a tidy little room.