• 18 Jun, 2025

Ya Zama Dole Gwamnatin Najeriya Ta Kawo Karshen Rashin Wutar Lantarki A Arewa—Cewar Atiku Abubakar

Ya Zama Dole Gwamnatin Najeriya Ta Kawo Karshen Rashin Wutar Lantarki A Arewa—Cewar Atiku Abubakar

1000005523.webp

Tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar ya nuna bacin ransa kan rashin wutar lantarki a arewacin Najeriya.

Atiku Abubakar wanda dan takarar shugaban kasa ne karkashin babbar jam'iyyar adawa ta PDP, ya bayyana cewa mahukunta sun jefa kasar cikin duhu.

Atiku Abubakar ya ce, akwai matakai da dama da yakamata gwamnatin kasar ta dauka domin kawo karshen matsakar rashin wutar lantarki amma hakan ya gagara.

Atiku ya yi kira ga masu hannu cikin harkar wutar da su gaggauta kawo karshen duhun da su ka jefa yan kasar a ciki musamman yankunan da babu wutar ko kadan.

Abubakar ya ce, akwai bukatar mika harkar samarda wutar lantarki zuwa hannun yan kasuwa na kwarai wadanda za su sa hannun jari da gaske domin kawo karshe matsalar.

Atiku Abubakar ya ce, akwai hanyoyin samarda wutar lantarki a kasar wadanda su ka hada da amfani da iska, da hasken rana da iskar gas da sauransu, wadanda duk Alkah ya azurta Najeriya da su, amma gwamnati ta ki amfani da su don kawo karshen matsalar rashin wuta.

Atiku ya kara da cewa, lokaci ya wuce da Najeriya za ta nace sai ta yi amfani da hanyar samarda wuta guda daya tilo.

Atiku ya bayyana cewa, matukar hanyar samarda wutar da Najeriya ke kai a yanzu za a dogara da ita, babu wani cigaba da za a gani a kasa nan da shekaru aru-aru masu zuwa.

Atiku Abubakar ya ce, yanada matakai na kawo canji ta fuskar samarda wutar lantarki a Najeriya. Atiku ya ce, yayi imani da matakan za su kawo cigaba idan ya samu damar zama shugaban kasa.

Abubakar ya ce, akwai sabbin tsare-tsare da ya ke da su don ganin matsalar wutar lantarki a kasar ta zama tarihi. Atiku ya ce, gwamnati mai ci ba ta da niyyar kawo karshen matsalar nan kusa.

 

Ahmed Abubakar

How puzzling all these changes are! I'm never sure what I'm going to turn into a tidy little room.