• 17 Jun, 2025

Ya Zama Dole Gwamnati Ta Kawo Karshen Matsalolin Najeriya—Cewar Gwamnonin Arewa 19

Ya Zama Dole Gwamnati Ta Kawo Karshen Matsalolin Najeriya—Cewar Gwamnonin Arewa 19

1000006240.jpg

A jiya ne gwamnonin arewa 19 suka gudanarda wani taron domin bitar matsalolin da ke addabar yankin da hanyoyin warwaresu.

Gwamnonin yankin sun bayyana cewa zanza-zangar da aka gudanar a watan Agusta kan rashin gwamnati mai nagarta gargadi ne ga gwamnatoci kan yadda lamura suka tabarbare a kasar.

Gwamnonin sun ce, talauci da yunwa da rashin aikin yi tsakanin matasa na daga cikin manyan matsalolin da suka sa matasan suka gudanar da zanga-zangar a wattannin baya da suka gabata.

Shugaban gwamnonin na arewa gwamnan Gombe Muhammadu Inuwa Yahaya ya ce, matasa na bukatar canjin lamura a kasar kuma ya zama dole su sauraresu.

Yahaya ya bayyana cewa ya zama dole gwamnonin arewa su duba lamuran da idon basira ta hanyar bawa matasan ilimi da ayyukan yi, yadda za su zama masu amfani a kasar.

Daga cikin wadanda suka halarci taron sun hada da Sarkin Musulmi Abubakar Sa'ad da shugaban rundunar tsaron kasar Christopher Musa da sauran kusoshin yankin arewa.

Taron ya kuma duba yadda tazara ke da akwai tsakanin yankin arewa da kudancin kasar ta fuskar tattalin arziki, inda masu taron suka bayyana cewa dole ne a yi wani abu akai.

Sun ce akwai bukatar bijiro da sabbin tsare-tsaren samarda ayyuka tsakanin  matasa da rage radadin talauci da ma sa hannun jari don amfanin yankin.

A karshen taron, shugabannin na arewa sunyi watsi da gyare-gyaren da gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ke kokarin yi, inda ya turawa majalisa kudurin nasa.

Shugabannin sun tattauna matsalar rashin tsaro da ke addabar yankin arewa kama daga Boko Haram zuwa matsalar yan bindiga da garkuwa da mutane.

 

 

Ahmed Abubakar

How puzzling all these changes are! I'm never sure what I'm going to turn into a tidy little room.