• 17 Jun, 2025

Ya Kamata Gwamnatin Tarayya Ta Dauki Mataki Kan Sabuwar Kungiyar Lakurawa Mai Mummunar Akida Kafin Lokaci Ya Kure—Cewar Wani Mazaunin Birnin Sakkwato

Ya Kamata Gwamnatin Tarayya Ta Dauki Mataki Kan Sabuwar Kungiyar Lakurawa Mai Mummunar Akida Kafin Lokaci Ya Kure—Cewar Wani Mazaunin Birnin Sakkwato

1000008398-1.jpg

Mazauna jihar Sakkwato a arewacin Najeriya sunyi nemi taimakon mahukunta daga tsangwamar wasu sabbin yan akidar da ake kira Lakurawa.

Yan jihar ta Sakkwato sun bayyana cewar yan kungiyar na musu barazanar rayuwarsu a jihar da ma jihar Kebbi.

Rundunar sojan Najeriya sun tabbatarda bullar yan akidar cikin al-ummar ta Sakkwato da Kebbi a arewa maso yammacin kasar, inda rundunar ta ce, bullar ta Lakurawa babbar kalubale ce a harkar tsaro a yankin.

Wani mazaunin birnin Sakkwato Malam Muhammadu Bauni ya bayyana cewa yan kungiyar ta Lakurawa na ikrarin kare al-ummar ne daga yan bindiga da ke addabar yankin.

Bauni ya ce, hankalinsu bai kwanta da yan Lakurawan ba, domin suna bijiro musu da wasu tsauraran dokoki a jihar.

Bauni ya ce kwanannan yan Lakurawan suka yi wa wasu daga cikin matasa mummunar duka sakamakon matasan sun aske gemunsu, insa suka daki masu sauraron wakoki.

Muhammadu ya ce, su Musulmai ne kuma basa adawa da dokokin Shari'ar Musulunci amma bai kamata ace akwai gwamnati a cikin wata gwamnati ba.

Muhammadu Bauni ya ce, babu wata Shari'ar da ta haramta aske gemu, amma yan Lakurawa suna dukan mutane sakamakon aske gemu.
 

Ahmed Abubakar

How puzzling all these changes are! I'm never sure what I'm going to turn into a tidy little room.