
Wata mawakiya kuma tsohuwar yar masana'antar shirya finafinai ta Nollywood daga kudancin Najeriya Onyeka Onwenu ta rasu.
Onwenu ta rasu ne bayan ta yanke jiki ta fadi jiya a wani dandali a birnin Eko yayin bikin zagayowar ranar haihuwar wata mai suna Stella.
Masoyan Onyeka Onwenu za su dade suna tunawa da ita saboda rawar da ta taka a masana'antar waka da finafinai a kudancin Najeriya.
Masoyan nata suna ta tura sakonnin jimamin rashin ta tun lokacin da aka sanar da mutuwar tata jiya Talata a wani asibiti a jihar Legas.
Rahotannin sunce, bayan Onyeka Onwenu ta yanke jiki ta fadi a tsaka da bikin shagalin zagayowar shekarar Stela, an garzaya da ita asibiti domin kulawa da ita, inda daga bisani tace ga garin ku.
Onyeka Onwenu dai na da baiwar zagin murya yayin da take raye a masana'antun wakoki da finafinai a Najeriya. Hakan ya sa ta samu gagarumin farin jini a Najeriya da ma wasu kasashen Afrika.
Onyeka Onwenu a baya ta bada wasiyyar cewa kada ayi mata bizina na almabazzaranci idan ta rasu. Maimakon haka, bayan ranta, ayi mata addu'a aci abinci kowa ya watse.