
Wata mata mai suna Alice Loksha ta tsira daga hannun 'yan kungiyar Boko Haram bayan ta shafe shekaru 6 tare da su.
Kungiyar Boko Haram sun yi garkuwa da Alice Loksha 'yar shekaru 42 tun shekara ta 2018, yayinda ta ke aiki da hukumar UNICEF a ofishinsu da ke garin Kala Balge a jihar Borno.
Manjo janar Wahdi Shuaibu ne ya sanarda tserewar Alice daga hannun Boko Haram sakamakon jajircewar rundunar hadin kai na sojojin Najeriya da ke arewa maso gabacin kasar.
'Yan kungiyar Boko Haram dai sun tilastawa Alice auran wani mai suna Abu Umar wanda ta haifi namiji tare da shi.
'Yan kungiyar sun sake tilasta mata auran wani kwamandan ISWAP Abu Simak bayan na farko gabanin tserewarta daga hannunsu.
Alice ta arce daga wani sansanin 'yan kungiyar ne mai suna Dogon Chuku a watan Oktoban wannan shekara, inda ta tsira zuwa hannun sojojin Najeriya a jihar Borno.
Wata mai suna Fayina Ali ita ma ta yi nasarar kubuta daga hannun wasu 'yan ta'addan bayan sun yi garkuwa da ita a shekara ta 2020, a hanyar Kaduna.
Yanzu haka dai matan biyu na samun kulawa da ya kamata daga rundunar sojojin Najeriya kafin a mika su zuwa iyalansu.