• 18 Jun, 2025

Wata Kungiya A Kaduna Ta Bayyana Yadda Za Ta Gudanar Da Zanga-Zanga

Wata Kungiya A Kaduna Ta Bayyana Yadda Za Ta Gudanar Da Zanga-Zanga

Wata Kungiya A Kaduna Ta Bayyana Yadda Za Ta Gudanar Da Zanga-Zanga

screenshot-20240727-132157-1722082966126.jpg

Wata kungiya daga jihar Kaduna mai suna "Northern Comrades Movement of Nigeria" a harshen turanci ta ce, sun sanar da hukumomin tsaro tsarin zanga-zangar da za su gudanar a birnin Kaduna.

Kungiyar ta ce ta sanar da hukumar tsaro ta DSS da rundunar 'yan'sandan jihar Kaduna da hukumar kare hadura ta FRSC da ma kungiyar 'yan jaridu.

Kungiyar ta ce zanga-zangar ta ta lumana ce ba ta tashin hankali ko karya doka da oda ba. Don haka, kungiyar tana neman hukumomin tsaron da su bawa 'ya'yanta kariya kamar yadda kundin tsarin mulkin kasa ya tanadar yayin gudanar da zanga-zangar ta lumana.

Kungiyar ta ce zanga-zangar ta neman samun saukin rayuwa ce ta wahala da talaka ke ciki da rashin gwamnati mai nagarta da lalacewar tattalin arzikin kasa karkashin shugaba Bola Tinubu.

Shugaban kungiyar na kasa Jibrin Ibrahim Yaro ya bayyana yadda zanga-zangar za ta gudana a birnin Kaduna daga farko zuwa karshe.

Ya ce, zanga-zangar za ta fara ne ranar 1 ga watan Agusta, inda za'a fara tattaki daga unguwar Kawo, titin Ahmadu Bello zuwa titin Kashim Ibrahim dab da gidan gwamnatin jihar ta Kaduna.

 

 

 

 

 

Ahmed Abubakar

How puzzling all these changes are! I'm never sure what I'm going to turn into a tidy little room.