• 18 Jun, 2025

Wata Farfesa Ta Maka Gidan Jarida A Kotu

Wata Farfesa Ta Maka Gidan Jarida A Kotu

aureclogos-2022-03-30t134229699-1.png

Wata Farfeasa mai suna Benedicta Daudu, ta jami'ar Jos wacce aka hukunta kan magudin jarrabawa a shekara 2016 ta maka gidan jaridar PREMIUM TIMES a kotu.

Farfesa Benedicta ta yi karar jaridar ne kan tuhumar bata suna a cikin wani rahoton da gidan jaridar ta rubuta akan ta.

Benedicta Dauda wacce yanzu haka malama ce a jami'ar jihar Taraba ta maka jaridar ne a babban kotun tarayya da ke birnin Abuja, inda ta ke kalubalantar abinda aka rubuta akan ta.

Jaridar PREMIUM TIMES dai ta ruwaito labarin cafke Dauda da laifin satar amsa yayin da ta ke rubuta jarrabawar zango na biyu a kokarinta na samun digiri ta biyu.
 

Ahmed Abubakar

How puzzling all these changes are! I'm never sure what I'm going to turn into a tidy little room.