• 17 Jun, 2025

Wata Dalibar Jami'ar Jihar Legas Ta Ce Hukumar Jami'ar Mazambata ne

Wata Dalibar Jami'ar Jihar Legas Ta Ce Hukumar Jami'ar Mazambata ne

1000010896.jpg

Wata dalibar jami'ar Jihar Lagas wato LASU ta zargi hukumar jami'ar da neman kudi har Naira dubu 260 daga hannun kowani dalibin jami'ar da sunan kudin rijistar kwasa-kwasan da dalibin ya fadi.

Da ta ke tattaunawa da kafar yada labarai, daya daga cikin daliban wanda ya kamata ta kammala karatunta tun shekara ta 2010 ta yi ikrarin cewar jami'ar ta hana ta yin rijistan kwasa-kwasan da ba ta ci ba shekaru 14 kenan.

Wasu daliban jami'ar sun nuna damuwarsu da yadda hukumar jami'ar ta lalace wajen neman kudade masu yawan gaske daga hannun daliban da sunan kudin rijista da yakai Naira 260,000.

Dalibar ta kara da cewa, ta roki hukumar jami'ar ta duba lamarin amma hakan ya ci tura, inda jami'ar ta dage sai sun biya kudaden kamar yadda ta bukata.

Matsalar ta shafi daruruwan daliban da ba su kammala karatun nasu ba kamar yadda wasu daga cikinsu suka shaidawa wata kafar yada labarai.

Daliban sun ce rashin adalci ne idan aka bukaci su biya wadannan makudan kudaden duba da cewa ba laifin su ba ne, domin jami'ar ce ta janyo jinkirin rashin kammalawarsu lokacin da ya kamata.

Wani dalibin ya ce, ya samu damammaki da dama na samun aiki, amma sakamakon rashin takardar shaidar kammala jami'ar a hannu, bai samu ko daya daga cikin ayyukan ba.

Mai magana da yawun jami'ar ta Jihar Legas Oluwayemisi Thomas-Onashile ta ce ba ta taba tunanin akwai daliban jami'ar da ke fuskantar wannan matsalar ba.

Oluwayemisi ta ce za ta gudanarda bincike domin gano ikrarin daliban gaskiya ne ko akasin haka.
 

Ahmed Abubakar

How puzzling all these changes are! I'm never sure what I'm going to turn into a tidy little room.