• 18 Jun, 2025

Wata Cuta Ta Hallaka Shanu 1000

Wata Cuta Ta Hallaka Shanu 1000

screenshot-20240803-141229-1722691720082-1722691734849.jpg

Al'ummar jihar Adamawa musamman makiyaya sun shiga damuwa sakamakon mutuwar dabbobi sama da 1000 a makwabtar su jihar Taraba.

An samu bullar cutar da ke halaka shanu a garin Gembu karamar hukumar jihar Taraba arewa maso gabashin Najeriya.

Cutar dabbobin ta fara shafar karamar hukumar Gashaka duka a jihar Taraban, inda cutar ta fara yaduwa karamar hukumar Toungo dake jihar Adamawa.

Karamar hukumar Toungo dai na iyaka da karamar hukumar Gashaka inda cutar ta bullo.

Yanzu haka cutar ta dabbobi ta hallaka shanu kimanin dubu daya. Sunan cutar Hermorhegic Septicaemia a harshen kimiyya.

Sakatare a ma'aikatar kula da dabbobi a jihar Adamawa Dr. Aminu Suleiman Mohammed yace, tuni likitocin dabbobin jihar sun fara aikin binciken domin daukan matakan gaggawa a Adamawa.
 

Ahmed Abubakar

How puzzling all these changes are! I'm never sure what I'm going to turn into a tidy little room.