• 17 Jun, 2025

Wasu Yara Kanana Da Aka Tsare A Kurkuku Sakamakon Zanga-Zangar Watan Agusta A Najeriya Sun Yanke Jiki Sun Fadi, Sun Suma A Kotu Saboda Rashin Cin Abinci

Wasu Yara Kanana Da Aka Tsare A Kurkuku Sakamakon Zanga-Zangar Watan Agusta A Najeriya Sun Yanke Jiki Sun Fadi, Sun Suma A Kotu Saboda Rashin Cin Abinci

1000007292.jpg


Haryanzu gwamnatin Najeriya na cigaba da tsare yara kanana sakamakon zanga-zangar da aka gudanar na rashin gwamnati mai nagarta a watan Agustan wannan shekarar.

Wasu daga cikin yaran na fama da rashin abinci mai gina jiki, amma duk da haka, gwamnatin Najeriya na tsare dasu.

Yayinda aka kai wasu daga cikin yaran kotu bayan an fidda su daga kurkukun 'yan'sandan kasar, wasu daga cikin yaran sun yanke jiki sun fadi, yayinda wasunsu suka suma a dakin babbar kutun tarayya da ke Abuja.

Yaran su fadi sun suma ne sakamakon azabtar dasu da jami'an 'yan'sandan kasar sukayi tsawon lokacinda suke tsare.

Akwai zargin an azabtarda yaran ne ta hanyar hanasu abinci da abinsha watanni uku da suka hannun 'yan'sandan kasar.

Yaran dai ba suda wani laifi ko kadan. Yunwa da rashin shugabanci mai nagarta ya fidda yaran zanga-zangar, amma gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ta cigaba ta tsare su da ma azabtarda su.

Wani alkali a babbar kotun tarayyar mai suna Emeka Nwite ne dai ya bawa 'yan'sandan kasar umarnin kamawa tare da tsare yaran batare da hakki ba.

A kowace kasa a duniya dan kasa na da 'yanci a kundin tsarin muki ya gudanarda zanga-zanga idan bai gamsu da yadda gwamnatin kasar ke gudanarda lamura ba.

Duk da haka, a Najeriya, gudanarda zanza-zanga ya zama kamar laifin kisa, inda duk lokacinda yan kasar suka yi zanga-zangar lumana don neman yancinsu ake kama su kamar karnuka a tsare.

Yan Najeriya dai sun gudanarda zanga-zangar ne a watan Agustan da ya gabata a Abuja da Kano da Legas da sauran biranen kasar sakamakon rashin tsaro da yunwa da talauci da talakawan kasar ke fama da su.

 

Ahmed Abubakar

How puzzling all these changes are! I'm never sure what I'm going to turn into a tidy little room.