• 18 Jun, 2025

Wasu Jihohin Najeriya Za Su Fiskanci Ambaliyar Ruwa Idan Aka Sako Ruwan Dam Daga Kasar Kamaru

Wasu Jihohin Najeriya Za Su Fiskanci Ambaliyar Ruwa Idan Aka Sako Ruwan Dam Daga Kasar Kamaru

fb-img-17266337630322029.jpg

Hukumar kula da Koguna da madatsun ruwa a Nqjeriya ta gargadi 'yan kasar game da yiwuwar sakin ruwan Dam na Lagdo da ke kasar Kamaru.

Hukumar ta ce Dam din lagdo da ke arewacin kasar Kamaru ya mamaye yankunan ruwaye na tsawon kilomita 586 .

Shugaban hukumar ta NIHSA Umar Mohammed ne ya bayyana haka a daidai lokacin da ambaliyar ruwa ke barazana a Najeriya.

Gargajdin ya zo ne daidai lokacin da ambaliyar Dam din Alau ta yi ta'adi a birnin Maiduguri cikin makonni biyu da su ka gabata.

Akwai bukatar jihohin Adamawa da Taraba da Benue da Bauchi da Anambra da Bayelsa da Delta da Edo da ma Rivers da Cross River su shirya domin tunkarar matsalar.

Mohammed ya ce ya zama dole jihohi kamar Adamawa da Benue da Kogi da ke kusa da koguna su yi aiki tare da  kananan hukumomin su da gwamnatin tarayya don aikin sa idanu kan motsin ruwan domin shirin rage tsananin sa.

 

 

Ahmed Abubakar

How puzzling all these changes are! I'm never sure what I'm going to turn into a tidy little room.