
Wasu daga cikin jihohin arewacin Najeriya sun fara yunkurin samarwa kansu wutar lantarki domin kawo karshen matsalar a yankunan nasu.
Wasu masana a fannin lantarki Ahmad Zailani da Ibrahim Ali a jihar Jigawa sun ce akwai bukatar jihohi su mallaki lantarkin gashin kansu domin kawo karshen matsalar da ba ta da karshe.
Masanan sun ce arewacin kasar na da dunbun arziki musamman hasken rana da iska da za a iya amfani da su don cimma nasarar samarda lantarki.
Zailani ya ce jihar Jigawa kadai na da irin wadannan albarkatun da za a yi amfani da su don haskaka kauyukan da ba su da lantarki.
Zailani ya ce, abinda ake bukata kawai shi ne hubbasa daga gwamnatoci ta hanyar gayyatar kamfanoni masu zaman kansu saboda a cimma nasara.
A daya hannun, Jihar Gombe ma ta yi nisa wajen shirye-shiryen samarwa kanta lantarkin da ya kai karfin megawatt 100 ta hanyar amfani da hasken rana.
Ismailq Uba-Misilli wanda babban daraktan yada labarai ne daga gidan gwamnatin jihar Gombe ya bayyana cewa, yunkurin gwamnatin jihar ya zama wajibi duba da yadda samarda wutar lantarki ta hanyar amfani da ruwa ya zama babbar matsala a Najeriya.
Ismaila ya kara da cewa tuni gwamnatin jihar ta sanya hannu kan yarjejeniya da kamfanin kasar Chana kan batun fara aikin samarda lantarkin.
Uba-Misilli ya ce samarda wutar zai kuma samarwa dunbun matasa ayyukan yi harma da janyo masu saka hannun jari a jihar baki daya.