
Yan Najeriya na kalubalantar kamfanin mai na gwamnati NNPCL kan rashin gaskiya wajen sayarda man fetur a kasar.
Hakan ya biyo bayan sanarwar da kamfanin ya yi cewar farashin litar mai zai kasance Naira 1,030 kwana biyu da suka gabata.
Yan kasar suna korafin cewa wasu daga cikin gidajen man yan kasuwa musamman a birnin tarayya Abuja na sayarda litar man fetur din Naira 1,025 wanda hakan kasa ne da yadda gidajen man kamfanin NNPCL ke sayarwa.
A Abuja babban birnin kasar an tabbatar wasu gidajen man fetur masu zaman kansu na sayar da litar man fetur kasa da yadda na gwamnati ke saidawa.
Gidan man Mobil da ke titin Ahmadu Bello a Abuja da ma wani gidan man da ke titin Obafemi Awolowo a Utaka, da gidan man Eterna na sayarda litar man Naira 1,050 zuwa 1,120, yayinda wasu ke sayarwa kasa da farashin kamfanin mai na gwamnati.
Yan Najeriya dai sun sa rai kudin litar man zai yi sauki yadda bazai gagari talakawan kasar ba amma hakan ya gagara, inda gwamnatin shugaba Tinubu ta kara kudin man sau biyu kasa da wata guda.