
Wasu daga cikin masu aikin a ma'aikatar ilimi ta tarayya sun bayyana dalilan da suka sa Farfesa Tahir Mamman ya rasa kujerarsa na ministan ilimin Najeriya.
Wasu da suka ce kada a ambaci sunayensu sun yi korafi kan korarren ministan kan rashin biyan bashin albashi da wasu ke bin ma'aikatan tunda Tahir Mamman ya hau kujerar mulki.
An kuma zargi ministan da dauki dori a jami'o'in kasar musamman jami'ar Abuja, inda ya tilastawa jami'ar amincewa da Farfesa Aisha Maikudi a matsayin shugabar jami'ar batare da al-ummar jami'ar na son hakan ba.
Ministan ya yi haka ne da hadin bakin tsohon shugaban jami'ar Farfesa Abdul-Rashid Na'Allah domin cimma bukatarsa.
Wani rahoto ya nuna cewa tsohon shugaban jami'ar Farfesa Na'Allah ya hada baki da korarren ministan wajen nada Aisha Maikudi domin biyan mahaifinta alherin da shima ya yi mishi na zama shugaban jami'ar ta Abuja shekaru biyar da suka gabata.
An tafka magudi da dama a jami'ar ta Abuja wajen nada shugabar Aisha Maikudi wanda ake zargin korarren ministan ilimin Tahir Mamman da hannu a ciki.