
Wani mai suna Kabiru Matazu wanda yayi ikrarin shi ne shugaban kungiyar matasan arewacin Najeriya, ya ce, matasan sun janye daga zanga-zangar da aka shirya za'ayi a kasar.
Ya ce, sun dauki matakin ne don tabbatar da zaman lafiya a yankin arewa da ma kasa baki daya.
Matazu ya ce, sun nisantar da kansu daga duk wata zanga-zanga da ake yunkurin farawa mako mai zuwa a fadin Najeriya.
Kabir Matazu ya bayyana cewa, sun lura zanga-zanga ba ita ce mafitar matsalolin kasar ba. Anyi zanga-zangar EndSAS a kudancin kasar amma babu wani canji mai ma'ana da aka samu.
Ya kara da cewa, tarihi ya nuna, an gudanar da zanga-zanga da dama a baya amma ba'a cimma wani abu ba.
Lokuta da dama a baya zanga-zanga tana rikidewa ta zama tashin hankali, inda ake rasa rayuka da dukiya.
Matazu ya ce, anyi zanga-zanga a kasashe irin su Libya da Syria da sauransu amma babu wani nasara da aka cimma, a karshe ma lalacewa kasar Libya tayi.