
Wani matashi mai shekaru 25 ya rasa ransa a birnin Legas bayan ya fada a cikin wuta.
Matashin ya fada a cikin narkakken karfe a wani kamfani ya hallaka kanshi.
Kawo yanzu dai babu cikakken bayani kan sunan matashin da ya kashe kansa.
Mai magana da yawun rundunar yan sandan jihar Legas SP Benjamin Hundeyin, ya ce sun samu rahoton mutuwar matashin daga karamin ofishin su da ke kan titin Sagamu.
Hundeyin ya ce Kamfanin na cikin rukunin kamfanonin da ke yankin Ikorodu a birnin na Legas.
Rahotanni sun ce abokan aikin mamacin sunyi kokarin dakatar da shi daga hallaka kansa amma hakan yaci tura.
Hundeyin ya ce jami'an yan sandan rundunar sun kai ziyarar gani da ido inda lamarin ya faru a kamfanin, kuma sun ce sun fara bincike akan iftila'in.