
Wani lawya a Najeriya Abeny Mohammed yace sakacin gwamnati wajen hana zanga-zanga faruwa ta hanyar sauraran korafe-korafen yan kasa shi ne babban kuskuren da gwamnatin ta yi.
Girke jami'an tsaro domin dakatar da masu zanga-zanga na nuna gazawar gwamnati kuma hakan ya nuna gwamnatin ba ta san bukatar mutane ba.
Lawyan yace amfani da karfi da shugaban kasa Bola Tinubu keyi akan talakawan kasa da sunan hana su zanga-zanga babban tauye hakkin dan adam ne a mulkin dimukuradiyya.
Abeny Mohammed ya kara da cewa amfani da kotu da wasu gwamnoni sukeyi don killace masu zanga-zangar neman hakkin su shima cin zarafi da tauye hakkin dan adam ne kamar yadda sashi 40 na kundin tsarin mulkin Najeriya ya tanada.
Mohammed yace abinda alkalan sukayi abin Allah wadai ne da rashin sanin makaman aikin alkalanci a Najeriya. Hada baki da sukeyi da shugabanni waje cin zarafin yan Najeriya abin takaici ne.