
Wani lauya mai zaman kanshi mai suna Inibehe Effiong dake birnin Eko yace sun shirya tsaf don tsayawa masu zanga-zanga a jihar Legas.
Lauyan mai rajin kare hakkin bil'adama ya bayyana cewa za su yiwa 'yan jihar ta Legas aiki kyauta idan jami'an tsaro suka kama wani yayin zanga-zangar.
Lauyan yace, taimakon nasu zai tsaya ne kan masu zanga-zangar gaskiya ba bata gari wadanda zasu fita tada hankali ko karya doka ba.
Lauyan ya kara da cewa, abin takaici ne yadda jami'an tsaro ke hada baki da jami'an gwamnati wajen kojarin hana mutane gudanar da zanga-zangar duk da cewa sun san yin hakan 'yancin 'yan kasa ne.
Lauyan yace, zanga-zanga na daya daga cikin 'yancin 'yan kasa wanda aka bayyana a cikin kundin tsarin mulkin Najeriya. Don haka, kamata yayi jami'an tsaro su kyale mutane su gudanar da zanga-zangar batare da wata tsangwama ba.