• 17 Jun, 2025

Wani Bincike Ya Gano Cewa Dan Wasan Kwallon Kafar Nan Vinicius Dan Asalin Kasar Kamaru Ne Ba Brazil Ba

Wani Bincike Ya Gano Cewa Dan Wasan Kwallon Kafar Nan Vinicius Dan Asalin Kasar Kamaru Ne Ba Brazil Ba

1000011992.jpg

Wani bincike da aka yi na kwayoyin halitta ya tabbatarda cewar dan wasan Brazil, Vinicius Jr. tushensa daga Kamaru yake.

Hukumar kwallon kafar Brazil ce ta yi binciken tare da hadin gwiwar masu gano yan asalin tsatson Afirka ranar Talata a Fonte Nova.

An bayyana sakamakon binciken ne gabanin wasan da aka buga na wasan neman shiga gasar cin kofin duniya, inda aka tashi 1-1 tsakanin Brazil da Uruguay.

Binciken ya gano cewar tsatson dan wasan na kungiyar kwallon kafar Real Madrid daga kabilar Tikar yake a Kamaru.

An bayar da takardar shaida ga Vinicius Jr. ta cewar daga Kamaru yake, tare da wani faifan bidiyo da ke nuna gadon kakanninsa na Tikar, wata fitacciyar kabila a Kamaru.

Wannan yunkurin wani bangare ne na sanin hakikanin tushe daga CBF, wanda ke girmama tarihi da na al'ummar bakaken fata yan asalin Brazil, tare da mayar da hankali na musamman kan kwallon kafa.

Da yake magana game da tushensa, Vinicius ya ce, gano cewa tsatsonsa yana daga Kamaru lokaci ne na musamman a gare shi da iyalina.

Dangane da binciken mahaifinsa, Vinícius ya nuna farin cikinsa, yana cewa yana da mahimmanci a gare mu mu san inda muka fito.

Ya kara da cewa, yawancin mutanen Brazil ba su da masaniya game da zuriyarsu ko gadonsu,.saboda haka, ya  yi farin ciki da cewa ya na da tushe a kasar Kamaru.

Vinicius ya sanya riga ta musamman mai dauke da tutocin Brazil da Kamaru a wasan da suka buga da Uruguay domin girmama kasar sa ta asali da ta haihuwa.

 

Ahmed Abubakar

How puzzling all these changes are! I'm never sure what I'm going to turn into a tidy little room.