• 18 Jun, 2025

Wani Asibitin Dubai Zai Bude Reshen Sa A Abuja

Wani Asibitin Dubai Zai Bude Reshen Sa A Abuja

american-hospital-dubai-to-open-in-abuja-1.jpg


Wani asibiti mai suna American Hospital Dubai ya shirya domin bude reshen sa a birnin tarayyar Najeriya Abuja.

Hakan ya biyo bayan bude reshen sa na farko a birnin Legas kwanakin kadan da suka gabata.

Asibitin zai taimaka wajen kula da masu jinya, inda zai saukaka wa marasa lafiya zuwa birnin Dubai domin karin kulawa.

American Hoapital Dubai zai tallafa wa masu jinya wajen samun takardar izinin fita Dubai da ke kasar UAE tare da daukar nauyin kudin jirgin sama da ma muhalli a birnin yayin kulawa da majinyaci idan bukatar hakan ta taso.

Asibitin ya ce, yana duba yiwuwar bude wasu rassan sa a wasu biranen Najeriya  domin fadada ayyukan su.

Wakilin asibitin a Najeriya  Dr Abdalla Al-Mandoos shi ne ya bude reshen asibitin da aka gina a birnin Legas tare da sa idon kwamishinan lafiya na jihar ta Legas  Farfesa Akin Abayomi wanda ya wakilci gwamnan jihar Sanwo-Olu.

Ahmed Abubakar

How puzzling all these changes are! I'm never sure what I'm going to turn into a tidy little room.