• 17 Jun, 2025

Wake Zai Ci Gaba Da Tsada A Najeriya—Cewar Masana

Wake Zai Ci Gaba Da Tsada A Najeriya—Cewar Masana

1000009187.jpg


Masana harkar noma sun ce, farashin wake a Najeriya ba zai sauka nan kusa ba sakamakon rashin waken yadda ya kamata.

Najeriya dai a baya ita ce kasar da ke kan gaba wajen samarda wake a fadin duniya, inda ta ke samarda kashi 58 cikin 100 na wake a duniya.

Masanan sun bayyana cewa, rashin waken na da nasaba da tashe-tashen hankula na 'yan bindiga, da rashin jituwa tsakanin makiyaya da manoma da ma rashin dabarun adana waken a kasar.

Wadannan na daga cikin manyan dalilan da ya kawo karanchin waken a Najeriya, inda za a ci gaba da fuskantar matsalar karancin nan gaba.

Shugaban kungiyar manoman jihar Kano Alhaji Abdulrashid Magaji Rimin Gado, ya ce, noman waken ya ragu sosai sakamakon rashin tsaro da sauyin yanayi.

Magaji ya ce, kashi 45 na waken da suke amfani da shi a jihar Kano ana shigo da shi ne daga kasar Nijar, yayinda Naira batada daraja wajen kasuwancin waken idan aka kwatanta da kudin Nijar.

Rimin Gado ya ce, yayinda ake cikin matsalar rashin darajar Naira a Najeriya, kwatsam sai kasar Nijar ta dakatarda shigoda waken da sauran kayan noma Najeriya.

Wadannan manyan dalilan ne za su ci gaba da hana farashin waken da sauran kayayyakin gona sauka kamar yadda ake tunani a kakar kayayyakin abinci a Najeriya.

Abdulrashida Rimin Gado ya ja hankalin gwamnatin tarayyar Najeriya da ta daukin matakan sa ido a farashin kayayyakin abinci domin rage radadin tsadarsu.

Wani dan kasuwa na kasa-da-kasa a kasuwar Dawanau da ke Kano Alhaji Musa Gawuna ya ce, rashin noman waken a da yawa a wannan shekarar na daga cikin dalilan da suka kawo tsadarsa.

 

Ahmed Abubakar

How puzzling all these changes are! I'm never sure what I'm going to turn into a tidy little room.