• 17 Jun, 2025

WAEC Ta Karrama Matashi Makaho Da Ya Yi Fice A Jarrabawa

WAEC Ta Karrama Matashi Makaho Da Ya Yi Fice A Jarrabawa

1000012390.jpg

Hukumar shirya jarabawa ta WAEC ta karrama dalibin da ke da matsalar gani amma ya yi fice a jarabawar shekara ta 2023 a jihar Kaduna.

WAEC ta bawa dalibin Obo Sylvester kyauta a lokacin taron ta na 62 a birnin Kaduna, arewa maso yammacin Najeriya.

Obo Sylvester wanda ke da burin karantan Sahari'a a Jami'ar Calabar da ke jihar Cross River, ya samu maki 250 a jarabawar JAMB, inda ya yi fice a jarabawar ta WAEC.

Yayinda ya ke bayani a wajen taron na WAEC, Obo Sylvester ya ce, makanta ba gazawa ba ce, domin mutum zai iya zama duk abinda ya ke so a rayuwa idan ya sa hankali kuma ya yi aiki tukuru.

Sylvester ya yi farin ciki, inda ya mika godiyarsa ga hukumar WAEC da ta samar masa da abubuwan da ya ke bukata domin rubuta jarabawar cikin sauki, kuma ya yi nasara.

Mataimakiyar gwamnan jihar Kaduna wadda ta wakilci gwamna, Dakta Hadiza Sabuwa Balarabe, ta ce, gwamnatin jihar Kaduna na aiki tukuru wajen bunkasa harkar ilimi, shi ya sa ma ta shirya taron domin buba abubawa da su ka shafi ilimi a jihar, a cewar Hadiza Balarabe.

Balarabe ta ce, gwamnatin jihar ta ware kashi 25 cikin 100 na kasafin kudin shekara 2023, domin bunkasa ilimi, inda ta ce, gwamnatin jihar ta yaba kokarin hukumar jarabawa ta WAEC dangane da kokarin ta na inganta ilimi ta hanyar yaki da magudin jarabawa da sauransu.

Gwamnatin jihar Kaduna a cewar mataimakiyar gwamnan Hadiza Balarabe, za ta bada gudumawar fili kyauta mai tsawo da fadin mita 7,500 ga hukumar WAEC domin cimma niyyar ta na bude cibiyar rubuta jarabawar kwamputa a jihar.

A nasa bangaren, wakilin hukumar WAEC ya yaba hubbasar hukumar ta su game da kokarinta wajen amfani da na'urar kwamputa wajen gudanarda ayyukanta na jarabwa da sauransu.
 

Ahmed Abubakar

How puzzling all these changes are! I'm never sure what I'm going to turn into a tidy little room.