• 17 Jun, 2025

Wadanda Cire Tallafin Man Fetur Ya Shafa Kai Tsaye Su Ne Suka Haddasa Wahalhalun Da 'Yan Najeriya Ke Ciki—Cewar Adeboye

Wadanda Cire Tallafin Man Fetur Ya Shafa Kai Tsaye Su Ne Suka Haddasa Wahalhalun Da 'Yan Najeriya Ke Ciki—Cewar Adeboye

1000010918.jpg

Shahrarren malamin addinin Kiriskan nan a Najeriya Adeboye na Majami'ar RCCG, ya ce wadanda ba sa son cire tallafin man fetur a kasar su ne suka haddasa wahalhalun da 'yan Najeriya ke ciki.

Adeboye ya kara da cewa wadannan marasa imanin ne suka lalata darajar Naira a kasa da ma duniya baki daya saboda keta.

Adeboye ya ce kokarinsa da na sauran 'yan Najeriya ta hanyar addua ne ya taimaki kasar, da a yanzu haka Dala daya ya kai darajar Naira 10,000.

Adeboye ya furta haka ne a wata huduba da ya yi cikin bidiyo, inda ya ce, matsalar Najeriya ba a zamanin mulkin Tinubu ta fara ba.

Adeboye ya ce, adduar da ya gudanar ita ce ta ceto kasar daga yiwuwar masifar da tafi wadda ake ciki, inda ya kashe makudan kudade wajen shigoda man fetur ne ya jefa kasar cikin matsala gabanin hawan Bola Tinubu kan karagar mulkin Najeriya.

Adeboye ya ce dole ne Najeriya ta shiga damuwar tattalin arziki da talauci tsakanin 'yan kasa idan gwamnati za ta rika kashe biliyoyin Nairori domin shigoda man fetur duk da munada matatun man a kasar da aka lalatasu da gangan.

Wannan ne babban dalilin a cewar Adeboye da ya sa da shugaba Bola Tinubu ya hau mulki ya sanarda cire tallafin man domin hana sayar man fetur daga kasashen duniya, ta hanyar bawa Dangote damar bude matatarsa domin tace man a gida.
 

Ahmed Abubakar

How puzzling all these changes are! I'm never sure what I'm going to turn into a tidy little room.