
Ministan Abuja Nyesom Wike ya ce umarnin shugaba Bola tinubu ya ke arwatarwa kan ginawa alkalan kasar gidaje da saya musu motoci.
Wike ya furta haka ne.sakamakon zarge-zargen da ake mishi da gwamnonin kasar kan gurbata kasa da rashawa ta hanyar ginawa manyan alkalan kotunan Najeriya gidaje da motocin alfarma.
Nyesom Wike ya ce ayyukan gina gidajen da sayan motocin na cikin kasafin kudin shekarar 2024 da mu ke ciki, inda ya ce aikinsa kawai sa idanu ne kan ayyukan domin ganin komai ya tafi daidai.
Nysom Wike ya bayyana hakan ne yayin zantawa na musamman da manema labarai a birnin tarayyar Najeriya Abuja.
Wike ya ce, ba tsarinsa ba ne ginawa alkalan kasar gidaje da saya musu motocin alfarma, shugaban kasa ne jagoran aikin.
Wike ya kara da cewa majalisar dokokin kasar na da masaniya kan aikin domin sun rantaba hannu akan aikin kuma shugaban kasa Bola Tinubu ya amince da kwangilar.
Wike ya ce, bayan majalisar dokokin kasa, majalisar zantarwa ma ta amince da shirin gina gidajen alkalan domin basu dukkan 'yanci da ya kamata domin gudanar da ayyukansu.