• 18 Jun, 2025

Tutar Sojojin Najeriya Ce Ba Ta Rasha Ba

Tutar Sojojin Najeriya Ce Ba Ta Rasha Ba

screenshot-20240806-164203-1722958958520-1.jpg

Masu lura da lamuran yau da kullum na kasa a Najeriya sun gano cewa ba tutar kasar Rasha masu zanga-zanga ke dagawa ba a kasar ba.

Wani kwararren Farfeasa a fannin ilimin aikin jarida a Najeriya Farooq Peroji na daga cikin wadanda suka gano cewa tutar ta sojan Najeriya ce ba ta Rasha ba a wani rubutu da aka wallafa a shafin jaridar Sahara dake kasar.

A makon da ya gabata ne masu zanga-zangar neman sauyi a birnin Kano dake arewa maso yammacin Najeriya ne suka fara daga turar mai launin tutar kasar Rasha.

Sojojin Najeriya dai sun fara kama masu daga tutar da ma wani tela mai dinka musu tutar a babban birnin kasuwancin arewacin kasar kano da laifin cin amanar kasa.

Amma daga bisani, aka gano cewa asilin launin tutar sojojin Najeriya ne masu zanga-zanga ke daga wa ba tutar kasar Rasha ba.

Ahmed Abubakar

How puzzling all these changes are! I'm never sure what I'm going to turn into a tidy little room.