• 17 Jun, 2025

Tunda Tinubu Ya Hau Kan Mulki 'Yan Najeriya Ba Su Amfana Da Kudaden Tallafin Man Fetur Da Iskar Gas Ba—Cewar Gwamnan Bauchi Bala Mohammed

Tunda Tinubu Ya Hau Kan Mulki 'Yan Najeriya Ba Su Amfana Da Kudaden Tallafin Man Fetur Da Iskar Gas Ba—Cewar Gwamnan Bauchi Bala Mohammed

1000011619.jpg

Gwamnan jihar Bauchi Bala Mohammed Abdulkadir ya kalubalanci gwamnatin tarayya dangane da yadda 'yan Najeriya  ba sa amfana da kudaden tallafin man fetur da iskar Gas kamar yadda aka saba a baya kafin zuwan Bola Tinubu.

Bala Mohammed ya ce, ya kamata gwamnatin kasar ta yi adalci wajen rabon arzikin kasa tsakanin jihohi da 'yan kasa ba tare da bambanci ba.

Gwamnan Bauchin ya furta haka ne a jiya Litini yayinda gwamnan da ministan kudin kasar Wale Edun su ka gana, gabanin taron tattalin arzikin kasa da za a yi nan gaba a jihar Bauchi.

Bala Mohammed ya ce, kalamunsan sun zama dole duba da yadda 'yan Najeriya ba sa gani a kasa daga arzikin albarkatun mai da na iskar Gas tun hawan Bola Tinubu karagar mulkin kasar.

Gwamna Bala ya kara da cewa abin al'ajabi ne kasancewar Najeriya daya daga cikin kasashe masu arzikin mai a duniya amma 'yan kasar ba sa ganin komai tun hawan Shugaba Tinubu kan mulkin Najeriya.

Bala Mohammed ya ce ya zama dole su yi magana saboda idan ba su yi ba, babu wadanda za su yi, kuma babu wanda zai san abinda ke faruwa.

Gwamnan Bauchi ya kara da cewa akwai bukatar gwamnatin tarayya ta kara azama wajen samarda man fetur a kasar da yin adalci wajen rarraba arzikin man ga kowani dan kasar.

 

Ahmed Abubakar

How puzzling all these changes are! I'm never sure what I'm going to turn into a tidy little room.