
Ministan birnin tarayya Nyesom Wike ya bi sahun gwamnonin Najeriya wajen sa hannu domin biyan sabon albashi mafi karanci na Naira 70,000.
Ministan ya bada umarnin fara biyan sabon albashin a karshen wannan watan ba tare da bata wani lokaci ba.
Biyan sabon albashin zai shafi dukkan ma'aikatan hukumar birnin tarayya Abuja kamar yadda ma'aikatan jihohin ke amfana.
Sakataren yada labarai na minista Nyesom Wike Anthony Odeh ne ya bayyana hakan a wata takarda da ya sa wa hannu kuma ya rabawa manema labarai a Abuja.
Rahotanni sun bayyana cewa Nyesom Wike ya amince da fara biyan sabon albashin ne bayan matsin lamba da barazanar da kungiyar kwadago reshen Abuja ta yi masa, inda ta yi alwashin rufe ayyuka a birnin baki daya idan ban fara biya ba.
Idan ba a manta ba shugaba Bola Tinubu ya sa hannu tare da amincewar 'yan majalisar kasar kan karin albashin na ma'aikata, inda tuni wasu jihohin su ka fara biya tun watan Satumba.
Hakan ya biyo bayan kai ruwa rana da aka yi tsakanin kungiyar kwadagon kasar NLC da gwamnatin tarayya, wanda a karshe aka yi nasarar samun mafi karancin albashi na Naira 70,000.