• 18 Jun, 2025

Tsohon Shugaban Kasa Jonathan Ya Shiga Birnin Jalingo Domin Taron Kusoshin Jam'iyyar PDP

Tsohon Shugaban Kasa Jonathan Ya Shiga Birnin Jalingo Domin Taron Kusoshin Jam'iyyar PDP

fb-img-17244943427469063.jpg

Gwamnan jihar Taraba Agbu Kefas ya marabci tsohon shugaban kasar Najeriya Goodluck Ebele Jonathan.

Kefas ya marabci Goodluck Jonathan ne a filin tashi da saukar jiragen sama na Danbaba Suntai da ke babban birnin jihar Jalingo.

Gwamnan jihar Kogi Usman Ododo na d cikin tawagar Gwamna Agbu Kefas a filin jirgin domin tarbar tsohon shugaban kasar.

Tuni  gwamnonin PDP da sauran masu ruwa-da-tsaki a jam'iyyar suka taru a jihar ta Taraba domin tattauna matsalolin jam'iyyar wadanda suka hada da matsalar jihar Rivers da sauransu.

Ana rade-radin cewar hankalin yan jam'iyyar ta PDP ya fara karkata kan yiwuwar dawo da tsohon shugaban kasar Jonathan domin yin takarar neman mulkin kasar karo na biyu a shekarar zabe ta 2027.

Ahmed Abubakar

How puzzling all these changes are! I'm never sure what I'm going to turn into a tidy little room.