
A yau Talata ne tsohon Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya je birnin Maiduguri, da ke jihar Borno, arewa maso gabashin Najeriya.
Buhari ya isa babbar birnin jihar Bornon ne domin jajanta wa mazauna Maiduguri babban birnin jihar dangane da iftila'in ambaliyar ruwa da ta afkawa jihar a watannin baya.
Jami'an gwamnatin kasar ciki harda mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima wanda dan asalin jihar Bornon ne da uwargidan shugaban kasa Remi Tinubu ne suka kai ziyarar jajantawa yan Maiduguri a watannin baya.
Tun lokacin tsohon Shugaba Muhammadu Buhari bai je ba, sai a yau Talata ne ya kai yasa ziyarar ta jajantawa.
Ko menene dalilinda ya sa tun lokacin da iftila'in ambaliyar ta faru Buhari baije Maidugurin ba? Tambayar da yan kasar musamman yan arewacin Najeriya da dama ke yiwa tsohon shugaban kasar Muhammadu Buhari.