
Kamfanin rarraba lantarki a Najeriya TCN ya fara haskaka jihohin arewacin kasar da ke cikin duhu kusan makwanni 2.
Rahotanni sun nuna cewa kamfanin ya fara dawoda lantarkin a jihohin Kano da Kaduna da Filato da Gombe bayan ya gyara tashar wutar 330kV ta Ugwuaji-Apir 1.
Anyi amfani da tashar ne domin taimakawa tashar Shiroro-Mando da ke da matsala sakamakon aikin bata gari.
Mai magana da yawu kamfanin lantarkin Ndidi Mbah shi ne ya tabbatarda dawowan wutar jiya misalin 4:56 na jiya da yammaci.
Sauran jihohin da suka samu wutar sun hada da Nasarawa da Benue da ma Jihar Bauchi a yankin arewacin kasar.
Mbah ya ce, TCN sun shirya tsaf don fara aikin gyaran tashar wutar ta biyu, inda TCN ta jibge kayan aikin batare da bata lokaci ba.
Yan yankin arewacin Najeriya sun kwana suna murnar diwoda wutar musamman lokacinda aka dawoda lantarkin a biranen Jos da Gombe da Benue da Nasarawa.
Wasu rahotanni kuma ya nuna cews babu lantarkin har yanzu a Kaduna sa Kano da Jigawa, wutar ta dawo ne a Jihohin Benue da Filato da Nasarawa kadai.