• 18 Jun, 2025

Taraba Da Adamawa Da Wasu Jihohin Najeriya Sun Cika Shekaru 33

Taraba Da Adamawa Da Wasu Jihohin Najeriya Sun Cika Shekaru 33

fb-img-17248246130066392.jpg


Jihar Taraba na daya daga cikin jihohin da tsohon shugaban sojan Najeriya janar Ibrahim Babangida ya kirkira domin kara yawan jihohin kasar daga 19 zuwa 30.

Yanzu haka dai jihar ta Taraba da ma sauran jihohin da aka kirkira a lokaci guda a jiya suke cika shekara 33 da kafuwa.

Idan ba a manta ba an kirkiri jihar Taraba ne daga tsohuwar jihar Gongola a ranar 27 ga watan Agustan shekarar 1991.

Wasu daga cikin jihohin da aka kirkira a 1991 sun hada da jihar Adamawa da Yobe da Jigawa da Kebbi da Kogi da sauransu.

Mutane da dama suna ganin cewa kirkirar karin jihohin babban ci gaba ne, yayinda wasu ke ganin akasin haka, domin babu ci gaban azo a gani tsawon shekaru 33 da kirkiran jihohin.

Wasu mutanen cewa sukayi Najeriya za ta fi ci gaba da jihohi 19 fiye da jihohi 30 ko 36 kamar yadda ake da su a yanzu.

Ahmed Abubakar

How puzzling all these changes are! I'm never sure what I'm going to turn into a tidy little room.