
Kamfanin mai na NNPCL ya ce tabbas sun yi amfani da Dallar Amurka wajen sayan tataccen man petur daga matatar man Dangote.
Kamfanin ya ce sun dauki matakin ne gabanin shirin gwamnati kasar na fara amfani da Naira a harkar kasuwancin mai a Najeriya.
Mai magana da yawun kamfanin NNPCL Olufemi Soneye ya ce yanzu dai farashin mai na hannun 'yan kasuwa ne ba gwamnati ba.
Soneye ya kara da cewa daga 1 ga watan Goma ne za su fara amfani da Naira a duk kasuwancin mai a Najeriya domin dawo wa da darajar kudin kasa.
Abin jira a gani dai shi ne shirin gwamnatin Najeriya na fara amfani da Naira wajen saya da sayarwa a fannin man petur ko akasin haka.