• 17 Jun, 2025

Sojojin Najeriya Sun Sace Wani Dan Majalisa Yayinda Ya Ke Jefa Kuria

Sojojin Najeriya Sun Sace Wani Dan Majalisa Yayinda Ya Ke Jefa Kuria

1000011145.jpg

Wasu 'yan bindiga sun yi garkuwa da dan majalisar dokokin jihar Ogun da ke kudu maso yammacin Najeriya.

Dan majalisar Lukman Adeleye wanda shi ne shugaban marasa rinjayi a majalisar ya shiga hannun 'yan bindigan ne a runfar jefa kuri'a lokacin zaben kananan hukumomin jihar.

Babban daraktan yakin zaben Lukman Adeleye Olujimi Oloja ne ya tabbatarda afkuwar lamarin, inda ya ce yanzu haka Adeleye na tsare a magarkamar sojoji.

An sace Lukman Adeleye ne yayinda ya ke jefa kuri'arsa ranar Asabar a runfar zabe mai lamba 15 a garin Ibefun da ke karamar hukumar Odogbolu a jihar ta Ogun.

Ana zargin dai wadanda su ka yi garkuwa da Adeleye sojojin Najeriya ne, inda su ka kai shi barikin soja da ke Ilese.

Binciken menema labarai ya nuna cewa wasu masu fada a ji ne a jihar ta Ogun  su ka sa aka kama shi domin wata bukatarsu.

Daraktan yakin zaben dan majalisar Oloja ya ce duk kokarinsu a saki Adeleye ya ci tura, inda aka tabbatar musu Adeleye bazai fita daga hannun sojojin ba sai bayan an kammala zabe.

Oloja ya gayawa magoya bayansu da sauran jama'a cewa Adeleye na cikin tsaro da koshin lafiya, kuma suna iya kokarinsu don ganin an sake shi.

Oloja ya ce abinda sojojin su ka yi abin takaici ne kuma barazana ce ga yancin dan majalisar na yin zabe a matsayin shi na dan kasa sa'annan dan jihar Ogun.
 

Ahmed Abubakar

How puzzling all these changes are! I'm never sure what I'm going to turn into a tidy little room.