
Jami'an tsaro a Najeriya sun fara aikin hadin gwiwa tsakanin sojoji da yan sandan kasar domin tarwatsa masu zanga-zanga a babban birnin kasar Abuja.
An ga yan sanda na harba barkonon tsohuwa kan masu zanga-zanga wadanda suka hallara a rana ta biyar domin nuna rashin amincewar su da yadda abubuwa ke gudana a kasar.
Yan Najeriya dai sun dage da nuna rashin jin dadin su kan yadda talakawan kasar ke fama da wahalan yunwa da talauci sakamakon cire tallafin mai da rashin darajar kudi a Najeriya.
Rahotanni sun nuna cewa rigimar tsakanin yan kasar da jami'an tsaro ta shafi masu shigewa a kan titi da masu shaguna a birnin, inda suke tserewa don gujewa barkonon tsohuwa.
Jami'an tsaron DSS sun kama shugaban wata kungiyar kare hakkin bil'adama mai suna Adaramoye Michael Lenin a yau litini yayin zanga-zangar.
An ga sojoji da dama a yau fiye da kwanaki hudu da suka gabata a cikin birnin tarayyar Abuja suna kokarin dakile zanga-zangar ta hanyar cin zarafin al'ummar kasar.