• 17 Jun, 2025

Shugabannin Masu Harkar Awaki Sunyi Korafi

Shugabannin Masu Harkar Awaki Sunyi Korafi

Shugabannin Masu Harkar Awaki Sunyi Korafi

screenshot-20240723-182108-1721755388032-1721755408341-1.jpg

Shugaban kungiyar masu safarar dabbobi daga arewa zuwa jihar Ebonyi Salisu Tijjani Baba, ya yabawa gwamnatin jihar wajen gina musu  rijiyar burtsatsi a kasuwar dabbobin.

Shugaban ya ce, hakan babban kokari ne daga gwamnatin jihar ta Ebonyi kuma su na mika godiyar su.

Shugaban ya ce, duk da haka, 'yan kasuwan dabbobin suna bukatar gwamnatin jihar Ebonyi ta gina musu hanya zuwa kasuwar dabbobin domin su na fama da matsalar rashin hanyar shigar da dabbobi.

Shugaban ya kara da cewa, 'yan safarar dabbobi su na bukatar a samar musu da ruwa wanda za su rika shayar da dabbobin.

Salisu Tijjani ya ce, kamar yadda mutane suke bukayar ruwa don su rayu, haka ma dabbobi suna bukatar ruwan sha idan sunci abinci don su rayu.

Shugaban ya ce, duba da cewa suna biyan kudaden haraji batare da jan kafa ba, akwai bukatar gwamnatin jihar ta Ebonyi ta dube su da idon rahama ta hanyar samar musu da abubuwan da suke bukata don inganta harkar kasuwancin dabbobin.

 

Ahmed Abubakar

How puzzling all these changes are! I'm never sure what I'm going to turn into a tidy little room.