• 17 Jun, 2025

Shugaban Najeriya Bola Tinubu Ya Tafi Taron G20 A Kasar Brazil

Shugaban Najeriya Bola Tinubu Ya Tafi Taron G20 A Kasar Brazil

1000011303.jpg

Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya tafi kasar Brazil domin halartan taron kasashe 20 wato G20 da za a fara yau a birnin Rio de Janeiro na kasar ta Brazil.

Za a gudanarda taron ne karo na 19, inda shugabannin kasashen 20 za su tattauna batutuwa da dama da suka shafi duniya baki daya.

Shugaban kasar Brazil Luiz Inacio Lula da Silva ne shugaban kungiyar ta G20 wanda shi ne zai bude taron kamar yadda aka saba.

Za a gudanar da taron ne a yau Litini 18 da gobe Talata 19 ga watan Nuwamban nan, inda kasashe masu tattalin arziki guda 20 da shugabannin kungiyar kasashen Turai (EU) da kungiyar kasashen Afrika (AU) da ma hukumomin kudi na duniya kamar IMF da Bankin duniya.

Taron na bana zai duba yadda za a yaki yunwa da yadda talauci ke barazana da rayuwar al-ummar duniya, da sauran batutuwa masu muhimmanci.

Ana sa rai shugaban Najeriya Bola Tinubu zai kulla yarjejeniya ta fuskar tattalin arziki yayin ziyarar.

Wasu daga cikin jami'an gwamnati da ke taka wa shugaba Bola Tinubu zuwa  wajen taron, sun hada da ministan harkokin kasar waje Yusuf Tuggar.

Sauran ministocin sun hada da Idi Mukhtar da Hannatu Musawa da Aliyu Sabi Abdullahi da babban Daraktan hukumar sirri ta NIA Mohammed Mohammed. 

Ahmed Abubakar

How puzzling all these changes are! I'm never sure what I'm going to turn into a tidy little room.