• 17 Jun, 2025

Shugaban Kasa BolaTinubu Na Da Hannu A Rikicin Siyasar Jihar Rivers—Cewar Asari Dokubo

Shugaban Kasa BolaTinubu Na Da Hannu A Rikicin Siyasar Jihar Rivers—Cewar Asari Dokubo

1000006325.jpg

Tsohon shugaban tsagerun Naija Delta Asari Dokubo ya zargi shugaban kasa Bola Tinubu da amfani da ministan Abuja Nyesom Wike wajen kawo rikicin siyasa a jihar Rivers.

Idan ba a manta ba Jihar Rivers na cikin rikicin siyasa wanda tsohon gwamnan jihar Nyesom Wike da Gwamna mai ci Fubara ke rigima.

Dokubo Asari ya furta haka ne a cikin wani shiri a tashar talabiji na Arise a yau Talata.

Asari Dokubo ya ce idan Tinubu da Wike suka kuskura suka cire Sim Fubara a kan kujerar mulkin jihar Rivers, tabbas wani abu zai faru.

Asari Dokubo ya yi Allah wadai da halin shugaban kasa Bola Tinubu kan tashin hankalin siyasa da ya haddasa a jihar ta Rivers.

Asari ya ce, a matsayinshi na mai fada aji a jihar, dole ne ya yi tsokaci kan jefa yan jihar Rivers cikin rigingimu da Tinubu ya ke yi ta hanyar amfani da tsohon gwamnan Nyesom Wike.
 

Ahmed Abubakar

How puzzling all these changes are! I'm never sure what I'm going to turn into a tidy little room.