• 17 Jun, 2025

Shugaban Kasa Bola Tinubu Ya Sauka A Birnin Riyadh Domin Taron Kasashen Musulmai Na Duniya

Shugaban Kasa Bola Tinubu Ya Sauka A Birnin Riyadh Domin Taron Kasashen Musulmai Na Duniya

1000009409.jpg

Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya sauka a filin tashi da saukan jiragen saman kasa-da-kasa na birnin Riyadh da ke kasar Saudi-Arabia.

Shugaba Tinubu ya tafi kasar Saudin ne domin halartar taro kasa-da-kasa na kungiyar kasashen Musulmai na duniya.

Najeriya dai ta zama daya daga cikin kasashen kungiyar ne bayan ta yi rigista a lokacin mulkin tsohon shugaban sojan kasar Janar Ibrahim Badamasi Babangida.

Ana gudanarda taron ne na kasa-da-kasa tsakanin kasashen Musulmai na duniya domin tattauna matsalolin da ke addabar kasashen na Musulmai a fadin duniya.

Kamar sauran tarurrukan duniya, ana gudanarda taron kungiyar kasashen Musulmai ne a kowani shekara.

Ahmed Abubakar

How puzzling all these changes are! I'm never sure what I'm going to turn into a tidy little room.