• 17 Jun, 2025

Shugaban Jami'ar Maiduguri Laminu Mele Ya Yaba Aikin Hukumar NUC

Shugaban Jami'ar Maiduguri Laminu Mele Ya Yaba Aikin Hukumar NUC

1000011611.jpg

Shugaban Jami'ar Maiduguri Farfesa Mohammed Laminu Mele ya marabci tawagar hukumar da ke kula da jami'o'in kasar NUC a Jami'ar ta Maiduguri.

Hukumar ta NUC ta je jami'ar ne domin bitar tsangayar koyarda aikin jarida wato Mass Communication a jiya Litini.

Shugaban jami'ar wanda mai kula da sashin karatun digirgir ya wakilta Farfesa Yakubu Mukhtar, ya ja hankalin tawagar ta NUC da su yi aikinsu bisa bin ka'idoji da inganci.

Farfesa Yakubu ya ce, jami'ar na shirye a kowani lokaci domin tabbatarda bada ilimi mai nagarta a tsangayar ta sauran tsangayoyin jama'ar baki daya.

Shugaban tawagar ta NUC Farfesa Agber Kwaghkoldo ya yaba Jami'ar ta Maiduguri da karrama tawagarsa da ta yi, inda ya yi alkawarin bada shawarwari da za su kawo ci gaban jami'ar.

Farfesa Kwaghkoldo ya ce bitar tsangayar koyon aikin jaridan.na daga cikin ayyukansu domin tabbatarda kayan   aiki da bada horo ga dalibai domin samarda 'yan jaridu masu inganci.

 

 

Ahmed Abubakar

How puzzling all these changes are! I'm never sure what I'm going to turn into a tidy little room.