• 17 Jun, 2025

Shugaban Dattawan Arewa Ya Gargadi Masu Yiwa Matatar Man Dangote Zagon Kasa

Shugaban Dattawan Arewa Ya Gargadi Masu Yiwa Matatar Man Dangote Zagon Kasa

Shugaban Dattawan Arewa Ya Gargadi Masu Yiwa Matatar Man Dangote Zagon Kasa

screenshot-20240727-135450-1722084925687-1722084943581.jpg

Shugaban kungiyar dattawan arewa Farfesa Ango Abdullahi ya gargadi masu yiwa matatar man Aliko Dangote zagon kasa a kokarin sa na kawo canji a harkan mai a kasar.

Ango Abdullahi ya mika gargadin nasa ne a babban birnin tarayya Abuja yayin da ya nuna damuwar sa kan cin kafar da wasu bata gari ke wa Aliko Dangoten.

Farfesa Ango Abdullahi ya ce hakan bazai haifarwa Najeriya da mai ido ba, domin harkar matatar mai ba amfanin Dangote ne kadai ba.

Ango Abdullahi yayi tsokaci ne kan shiga tsakani da gwamnatin tarayya ke yi cikin kiki-kakar da ke faruwa tsakanin Aliko Dangote da masu ruwa da tsaki a harkar mai a Najeriya.

Idan ba'a manta ba wasu masu hannu a harkar mai a kasar sun sa wa Aliko Dangote kahon zuka kan katafaren matatar mai da ya gina a birnin Eko don ganin bai ci gaba ba.

Ahmed Abubakar

How puzzling all these changes are! I'm never sure what I'm going to turn into a tidy little room.