
Kungiyar addinai a Najeriya sunyi kira da jama'a su janye zanga-zangar don kaucewa kawo koma baya a kasar.
Sarkin Musulmi Sultan of Sokoto Alhaji Muhamnad Sa'adu Abubakar III da Shugaban Kiristocin kasar Archbishop Daniel Okoh ne suka yi kiran.
Shugabannin addinan biyu sunce sun kula da cewa zanga-zangar bazai haifawa yan Najeriya abin arziki ba sabanin lalata kasa.
Shugabannin addinan sun bayyana bacin ran su inda suka ce zanga-zangar da aka fara da sunan lumana ya juya tashin hankali.
Sun bayyana cewa, cikin awowi kadan zanga-zangar ta barke zuwa kone-kone da sace-sace da ma rasa rayuka.
Kungiyar shugabannin addinan sun gamsu da korafin yan Najeriya kan matsalolin talauci da yunwa da sauransu, amma akwai bukatar akai hankali nesa.
Shugabannin addinan sunyi kira ga jami'an tsaro da suyi taka-tsan-tsan yayin gudanar da ayyukan su. Sunyi kira da gwamnati su duba bukatun yan kasa.