• 17 Jun, 2025

Shugaba Tinubu Ya Ce Duk Wanda Bai Amince Da Sakamakon Zaben Jihar Ondo Ba, Zai Iya Zuwa Kotu

Shugaba Tinubu Ya Ce Duk Wanda Bai Amince Da Sakamakon Zaben Jihar Ondo Ba, Zai Iya Zuwa Kotu

1000011277.jpg

Shugaba Bola Tinubu ya ce duk wanda bai gamsu da Sakamakon zaben gwamna da aka gudanar a jihar Ondo ba ya je shi kotu.

Yayinda ya ke taya sabon gwamnan jihar murnar nasara, shugaba Tinubu ya yaba yadda aka gudanarda zaben cikin lumana ba tare da tashin hankali ba.

Shugaban kasa ya yabawa hukumar zabe mai zaman kanta INEC kan jajircewa wajen gudanarda zaben.

Jami'in Hukumar zaben Farfesa Olayemi Akinwumi ne dai ya sanarda Ayedatiwa na jam'iyyar APC a matsayin wanda ya lashe zaben da kuri'u 366, 781, yayinda dan takarar jam'iyyar adawa ta PDP Agboola Ajayi ya tsira da kuri'u 117, 845.

Shugaban kasa Bola Tinubu ya yaba wa 'yan takara 17 da suka nemi kujerar daga jam'iyyoyi daban-daban, sakamakon  dottako da suka nuna.

Shugaba Bola Tinubu ya yaba wa Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta INEC, kan kokarin dora Sakamakon zaben fiye da kashi 98 cikin 100 a kan manhajar hukumar a ranar da aka gudanarda zaben.

Tinubu ya kuma yaba kokarin jami'an 'yansanda da jami'an hukumar kare hadura da masu yiwa kasa hidama lokacin zaben.
 

Ahmed Abubakar

How puzzling all these changes are! I'm never sure what I'm going to turn into a tidy little room.