• 17 Jun, 2025

Shugaba Tinubu Ya Bi Tsarin Mulki Kafin Nada Sabon Hafsan Sojan Kasa—Cewar Christopher Musa

Shugaba Tinubu Ya Bi Tsarin Mulki Kafin Nada Sabon Hafsan Sojan Kasa—Cewar Christopher Musa

1000007563.jpg

Shugaban rundunar tsaron na sojan Najeriya Janar Christopher Musa ya ce nadin shugaban sojan kasa na rikon kwarya da Shugaba Bola Tinubu yayi babban cigaba a tarihin rundunar sojan Najeriya.

Musa ya bayyana cewa tsarin mulkin Najeriya ya bawa Shugaban kasa  hurumi da ikon yin hakan tunda shi ne babban kwamandan dukkan hafsan sojan Najeriya.

Christopher Musa ya furta haka ne a hedikwatar tsaron Najeriya da ke Abuja yayinda sabon shugaban sojan Manjo Janar Olufemi Oluyede ya kama aiki a ranar Juma'a.

Shugaban kasa Bola Tinubu ya nada sabon hafsan sojan ne ranar Laraba a matsayin mai rikon kwarya, kafin Laftanar Janar Taoreed Lagbaja ya dawo daga jinya.

Musa ya yi wannan bayanin ne yayinda cece-kuce ya yi yawa a cikin rundunar sojan kasar, inda rundunar ke ganin nadin da shugaba Tinubu ya yi bai bi ka'ida da al-adar rundunar sojaojin ba.

Musa ya ce, babu wani abin tada hankali a cikin nadin sabon hafsan sojan saboda shugaban kasa ya bi dukkan tanade-tanade na tsarin mulkin Najeriya kafin nada sabon hafsan sojan.

 

Ahmed Abubakar

How puzzling all these changes are! I'm never sure what I'm going to turn into a tidy little room.