
Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya bayyana dalilan da suka sa salon mulkinsa ke da tsauri ga yan Najeriya.
Tinubu ya furta haka ne a jiya litini a kokarin sa na jan hankalin yan kasar domin su fahinci manufofin gwamnatin nasa.
Shugaban ya yi kira da yan kasar da sukara bashi goyon bayan don cimma nasara a yunkurinsa na kawo sauyi mai ma'ana a Najeriya.
Tinubu ya nemi hadin kan sassan gwamnatin kasar da ma masu zaman kansu su taimakawa tafiyar tasa domin kasar ta tafi kafada-da-kafada da sauran kasashen duniya ta fannin cigaba.
Shugaba Bola Tinubu ya furta hakan ne yayinda yaje jawabi a taron tattalin arzikin kasa karo na 3o a birnin tarayya Abuja.
Shugaba Tinubu wanda mataimakinsa Kashim Shettima ya wakilta ya ce, tsare-tsaren farfado da tattalin arzikin kasa bisa jagorancin sa zai kawo wa kasar alfanu matuka musamman ta fannin tattalin arziki.