• 18 Jun, 2025

Shugaba Tinubu Ya Bayyana Dalilan Da Suka Sa Gwamnatin Sa Ke Da Tsauri

Shugaba Tinubu Ya Bayyana Dalilan Da Suka Sa Gwamnatin Sa Ke Da Tsauri

1000002139-1.webp

Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya bayyana dalilan da suka sa salon mulkinsa ke da tsauri ga yan Najeriya.

Tinubu ya furta haka ne a kokarin sa na jan hankalin yan kasar domin su fahimci manufofin gwamnatin nasa.

Shugaban ya yi kira da yan kasar da su kara bashi goyon baya don cimma nasara a yunkurinsa na kawo sauyi mai ma'ana a Najeriya.

Tinubu ya nemi hadin kan sassan gwamnatin kasar da ma masu zaman kansu su taimakawa tafiyar tasa domin kasar ta tafi kafada-da-kafada da sauran kasashen duniya ta fannin cigaba.

Shugaba Bola Tinubu ya furta hakan ne a jawabin taron tattalin arzikin kasa karo na 3o a birnin tarayya Abuja.

Shugaba Tinubu wanda mataimakinsa Kashim Shettima ya wakilta ya ce, tsare-tsaren farfado da tattalin arzikin kasa bisa jagorancinsa zai kawo wa kasar alfanu matuka musamman ta fannin tattalin arziki.

Ahmed Abubakar

How puzzling all these changes are! I'm never sure what I'm going to turn into a tidy little room.