• 17 Jun, 2025

Shugaba Tinubu Ya Bada Umarni A Ci Gaba Da Turawa Jihar Rivers Kudadenta

Shugaba Tinubu Ya Bada Umarni A Ci Gaba Da Turawa Jihar Rivers Kudadenta

1000012658.jpg

Gwamnatin Bola Tinubu ta yi amai ta lashe, inda ta bada Umarnin ci gaba da turawa jihar Rivers kudadenta daga asusun tarayya kamar yadda doka ta tanadar.

Rigima tsakanin gwamnan jihar Sim Fubara da mai gidansa ministan Abuja Nyesom Wike ce ta sa aka dakatarda turawa jihar kudadenta.

Mai magana da yawun babban akawun tarayya Bawa Mokwa ya ce, an dakatarda turawa jihar Rivers kudadenta ne sakamakon umarnin kotu, wanda ya dakatarda babban bankin Najeriya CBN da gwamnatin tarayya bawa jihar kudadenta na wata-wata.

Bawa Mokwa ya ce, daga yanzu za a ci gaba da turawa jihar Rivers kudadenta kamar kowace jiha bisa tanadin dokar kasa.

Kotun daukaka karar da ke birnin tarayya Abuja ce ta bada umarnin ci gaba da turawa jihar Rivers hakkinta, bayan ta soki hukuncin kotun tarayya na hana jihar samun kudadenta daga asusun tarayya.

Mai Shari'a Hamma Barka ya ce, za a sanarda ranar da kotun daukaka karan za ta yanke cikakken hukunci kan batun.
 

Ahmed Abubakar

How puzzling all these changes are! I'm never sure what I'm going to turn into a tidy little room.