
Yar fafutukar kare hakkin bil'adaman nan a Najeriya Aisha Yusufu ta ce Shugaba Bola Tinubu ba mutumin kirki ba ne ko kadan.
Aisha bayyana cewa babu yadda za a yi mutumin kirki ya zuba idanu ya na gani miliyoyin yan kasa na shan wahala amma ya gaza kawo karshen matsalolin kasar.
Aisha Yusufu ta tofa albarkacin bakinta ne a daidai lokacin da dan majalisar dattawa daga jihar Borno ta kudu Sanata Ali Ndume ya yi korafin wahalhalu da Shugaba Tinubu ya jefa talakan Najeriya cikin.
Ali Ndume ya bayyana cewa maimakon gwamnatin na Tinubu ta maida hankali wajen maganin hauhawan farashin kayayyakin abinci da man fetur da sauransu, gwamnatin ta yi biris da lamuran.
Ali Ndume ya shawarci Shugaba Bola Tinubu da ya gaggauta kawo karshen matsalolin kasar da suka addabi talaka kafin lokaci ya kure masa.
Ndume ya ce, yawancin magidanta a kasar musamman a jihar sa ta Borno ba sa iya cin abinci koda sau daya ne a rana sakamakon masifar tsadar abincin da sauran ababen rayuwa na yau da kullum.
A nata bangaren, Aisha Yusufu ta yi tsokaci kan korafin sanata Ali Ndume inda a shafin sada zumunta na X ta ce Tinubu ba mutumin karki ba ne.
Aisha Yusufu ta kara da cewa babu amfanin boye-boye game da halin Shugaban kasa. Magana ta gaskiya a cewar ta ita ce, Tinubu ba mutumin kirki ba ne.