• 17 Jun, 2025

Shugaba Bola Tinubu Ya Yiwa Hafsan Sojojin Najeriya Karin Girma

Shugaba Bola Tinubu Ya Yiwa Hafsan Sojojin Najeriya Karin Girma

1000008398.jpg

Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya kara wa hafsan sojan kasa na rikon kwarya Olufemi Oluyede girma zuwa matsatin Laftanar Janar na soja.

An gudanarda ganawar karin girman ne a faradar Shugaban kasa da ke birnin tarayya Abuja a jiya Talata.

Mai magana da yawun shugaban kasa Bayo Onanuga ya yabawa jajircewar rundunar sojan Najeriya na nuna kishin kasa da aiki tukuru domin tsaron kasa.

Shugaba Tinubu a cewar Bayo Onanuga ya ce, yana sane da kokarin da Olufemi Oluyede ya ke yi don ganin ya kawo tsaro a fadin Najeriya.

Shugaba Bola Tinubu ya bayyana cewa kofofin gwamnatinsa a bude suke don karban shawarwari daga rundunar sojan kasar domin tabbatarda tsaro a kasa.

Bola Tinubu ya ce, nasarorin da aka samu wajen yaki da yan ta'adda da yan bindiga na da nasaba da hubbasa da rundunar sojan kasa ta bada.

A nasa furucin, Laftanar Janar Oluyede ya nuna farin cikinsa da karin girman da shugana Tinubu ya mishi, inda ya ce, ya yi alkawarin ci gaba da aiki kan manufofin tsohon shugaban sojan Taoreed Lagbaja, ta hanyar wanzarda zaman lafiya a fadin Najeriya.

Oluyede dai ya shiga aikin sojan Najeriya ne a ranar 19 ga watan Satumban shekara 1992. Oluyede ya sha gwagwarmaya a cikin rundunar sojan kasar kafin wannan lokaci da ya samu damar jagorantan rundunar ta kasa baki daya.
 

Ahmed Abubakar

How puzzling all these changes are! I'm never sure what I'm going to turn into a tidy little room.