
Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya kori shugaban gudanarwa na jami'ar kiwon lafiya ta Otukpo da ke jihar Benue, Ohieku Mohammed Salami.
Korar Salamin na kunshe ne a cikin wata takarda da mai magana da yawun shugaban kasan Bayo Onanuga ya rabawa manema labarai jiya Laraba.
Hakan ya biyo bayan rashin da'a da Mohammed Salamin ya yi, wanda ya hada da dakatarda shugaban jami'ar ba tare da bin ka'ida ba.
Salami ya aiwatarda hakan ne duk da gargadinsa da ma'aikatar ilimi ta yi, amma ya yi kunnen uwar shegu.
Onanuna ya bayyana cewa Salami ya nuna halaye marasa kyau, ciki harda yi wa daraktocin ma'aikatar ilimin kasa barazana.
A watan Oktoba ne aka dakatarda shugaban jami'ar ta farko Farfesa Innocent Ujah sakamakon rashin da'a da rashin bin dokoki.
A daya bangaren kuma, shugaban kasa ya kori hukumar gudanarwa ta jami'ar Nnamdi Azikiwe da ke Awka a jihar Anambra, tare da sabon shugaban jami'ar Bernard Odoh da rijistra.